DARAJOJI 40 GA MAI YIN SALATI GA MANZON ALLAH (SAW).
DARAJOJI 40 GA MAI YIN SALATI GA MANZON ALLAH (SAW).
Kamar yadda Ibnul Qayyim ya kawo a cikin littafin sa, da ya wallafa akan salati ga Annabi saw, mai suna Jala’ul afham.
1). Yin salati Bin umarnin Allah ne.
2). Koyi da Allah swt, shima yana yiwa Annabi saw. salati
3.) koyi da Mala’iku, suma suna salati ga Annabi saw .
4). Samun lada goma.
5). Samun daraja goma.
6.) yafe laifi goma.
7.) Amsa adduar wanda ya fara da salati.
8.) samun ceton Annabi saw .
9.) Gafarta zunubin mai yawan salati .
10.) Allah zai yaye, masa abinda yake damunsa.
11). Zaiyi kusa da Annabi saw. Ranar Alkiyama
12). Wanda yayi salati ya sami ladan Sadaka.
13). Salati sababi ne na biyan bukata.
14). Allah taala Zaiyi salati ga wanda ya yiwa Annabi saw, salati.
15) Salati ga Annabi saw, yana tsarkake mai yawan yinsa.
16). Zai sami bushara da Aljannah.
17). Tsira daga tsananin kiyama
18). yiwa Annabi saw salati yana tuno maka abinda ka manta
19). salati yana cikin hakkokin Annabi saw.
20). Salati yana kamsasa majalisi.
21).Salati yana korar talauci.
22). Salati ga Annabi saw yana kore rowa .
23). Bazaa durmaza hancin mai salati ba.
24). Mai salati ya kama hanyar Aljannah.
25). Idan akayi taro aka tashi babu salati, zaayi warin mushen jiki.
26).A fara magana da yabo ga Allah da salati ga Annabi saw.
27). samun haske akan siradi ranar Alkiyama
28). fita daga Jafa’i, na laifi, idan anyi salati.
29).Mai yawan salati ga Annabi saw, yana samun yabo da girma.
30). samun Rahma
31). soyayyar Annabi saw, ga mai salati
32). Annabi saw ya Nuna yana son mai masa salati.
33). Samun shiriya da rayuwar zuciya .
34). Duk mai yiwa Annabi saw salati, ana gayawa Annabi saw, sunan sa.
35). Tabbata akan siradi ranar Alkiyama
36). Yiwa Annabi saw, salati, rokon Allah, kuma ibada ne.
37).Salati ga Annabi saw godiya ne ga Allah.
38). salati ga Annabi saw zakka ne da tsarki ga mai yawan yi.
39). Salati ga Annabi saw yana sa albarka ne ga jikin mai yi.
40). Salati ga Annabi saw, bushara da Aljannah kafin mutuwa.
ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYIDNA MUHAMMADIN ADADA MAFI ILMULLAHI SALATAN DAA'IMATAN BIDAWAAMI MULKILLAH.
KACE YA ALLAH KAYI SALAATI GA SHUGABAN MU MUHAMMADU ADADIN ILMIN ALLAH, SALATI DAWWAMAMMIYA (HAƊAƊƊIYA) DA DAWWAMAR (HAƊUWAN) MULKIN ALLAH.
(Wanda ILMIN ALLAH DA DAWWAMAR MULKIN ALLAH BASUDA IYAKA)
Wanda Sharifi Jikan Manzon Allah Imam Muhammad Bin Suleiman yace wannan 1 daidai yake da salatai 600,000 ga manzon Allah.
Allah YASA MU DACE
Comments
Post a Comment